Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hatsarin Jirgin Sama: Yadda Minista Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Najeriya


Ministan makamashi, Adebayo Adelabu
Ministan makamashi, Adebayo Adelabu

Rahotanni sun ce jirgin mallakin kamfanin Aero ya kusa faduwa ne a kusa da filin tashin jirage na Samuel Ladoke Akintola da ke Ibadan a jihar Oyo.

Ministan makamashi a Najeriya, Adebayo Adelabu, ya tsallake rijiya da baya, bayan da jirgin saman da yake dauke da su ya kusa faduwa.

Adelabu ya taso ne daga Abuja zuwa Ibadan babban birnin jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya a ranar Juma'a.

Gidan talbijin na Channels ya ruwaito cewa jirgin mallaki kamfanin Aero ya kusa faduwa ne a kusa da filin tashin jirage na Samuel Ladoke Akintola da ke Ibadan.

Rahotanni sun ce jirgin ya samu tangarda ne yayin da yake shirin sauka da misalin karfe 10 na daren Juma’a, amma ya kauce hanya ya fada daji.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa, ya fadawa Channels cewa mutum biyu ne a cikin jirgin – wato ministan da kuma matukin jirgin.

Babu dai wanda ya samu rauni a hatsarin, amma rahotannin sun nuna cewa wani sashen jirgin ya lalace sanadiyyar faduwar da ya kusa yi.

Jaridar Daily Trust wacce ita ma ta dauki labarin, ta ce gabanin aukuwar hatsarin, Hukumar Kula da Yanayi ta NiMET a Najeriya ta ba da gargadi kan hadarin da ke tattare da tafiya a wannan lokaci saboda hazo da ya lullube sararin samaniya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG