Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Iyalan Sojojinmu Da Suka Rasu Ba Za Su Tagayyara Ba - Babban Hafsan Hafsoshin Sojin Saman Najeriya


Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Saman Najeriya Air Marshal Hassan Bala Abubakar Ya Ziyarci Iyalan Dakarun Da Suka Rasu A Fagen Daga A Neja
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Saman Najeriya Air Marshal Hassan Bala Abubakar Ya Ziyarci Iyalan Dakarun Da Suka Rasu A Fagen Daga A Neja

A ranar Laraba, babban hafsan ya sauka a birnin Fatakwal inda ya yi tattaki har gidajen mamatan don yi wa iyalansu ta'aziyya.

ABUJA, NIGERIA - Babban hafsan hafsoshin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Marshal Hassan Bala Abubakar, ya ziyarci iyalan hafsoshin saman da su ka rasu yayin hatsarin jirgin saman mayakan a jihar Neja.

A ranar Laraba, babban hafsan ya sauka a birnin Fatakwal inda ya yi tattaki har gidajen mamatan ya kuma yi ta'aziyya ga iyalansu.

Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Saman Najeriya Ya Ziyarci Iyalan Dakarun Da Suka Rasu
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Saman Najeriya Ya Ziyarci Iyalan Dakarun Da Suka Rasu

Air marshall Abubakar wanda ya bayyana cewa wannan babban rashi ne dake zama koma baya ga rundunar sojojin sama da zai dauki rundunar shekaru kafin ta cike gurbin, ya ce ba za a bar iyalan mamatan su tagayyara ba.

Babban hafsan hafsoshin ya yi bayanin cewa sadaukar da rayuwarsu da sojojin suka kai ba zai taba zama asara ba, ya ce rundunar da sauran ‘yan Najeriya zasu ci gaba da tunawa da su.

Idan za a iya tunawa, jirgin saman sojoji samfurin MI 171E ya yi hatsari ne a ranar goma sha hudu ga watannan na Agusta a jihar Niger, yayin da yake kwaso gawarwakin sojojin da suka rasu da wadanda suka samu raunuka a fagen daga a jihar Neja.

Sunayen mayakan saman da su ka rasu a hatsarin:

1.Flight Lieutenan Adamu Ibrahim

2. Flight Lieutenant Anthony Duryumus

3. Lance Corporal Brigs Stephen peter

4. Lance Corporal Alaribe Daniel

5. Lance Corporal Jauro Amos

6. Lance Corporal Abdulrahman Abubakar

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG