Yansandan Iraq sun ce mayaka sun kutsa harabar ofishin gwamnatin lardi yau Talata suka kashe mutane takwas suka kuma raunata wadansu 15.
Shaidu sun ce maharan sun tada boma bomai a cikin wadansu motoci biyu da suka girke kusa da kofar shiga ofishin da dake Baquba babban birnin lardin Diyala.
Jami’an tsaro sun ce wadansu maharan sun shiga harabar suka bude wuta.Rahotanni na nuni da cewa, an yi garkuwa da wadansu sai dai ba a bayyana adadin wadanda aka yi garkuwa da su ba. Babu kuma tabbacin ko an shawo kan lamarin.
Kawo yanzu babu kungiyar da ta dauki alhakin kai harin An kai harin ne a daidai lokacinda majalisar lardin ke zamanta na mako mako. Harin ya kara sa kila-wa-kala dangane da karfin dakarun tsaron Iraq yayinda Amurka ke shirin janye dakarunta a cikin ‘yan watanni masu zuwa.