‘Yan bindigar al-shabab da mazauninta ke Somali sun kai hari kan masaukin baki dake wurin da ake kira Bisharo, a karamar hukumar Mandera. Sun yi amfani da gurneti da kuma wasu ababen fashewa, a cewar kwamandan yankin Job Boronjo.
Boronjo yace “lallai an kai hari, kuma ma’aikatan agaji na kan aiki yanzu haka.
Ba tare da bata lokaci ba kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin kai harin a kafar yada labaranta. Ta ce ta kai harin ne a kan kristocin da suke aiki a wurin.
Harin da aka kai yau Talata shine na baya-bayan nan a jerin hare haren da al-Shabab ta kai tsallaken iyaka, tun bayan da kasar Kenya ta kutsa cikin rikicin da ake yi a Somaliyya a shekarar 2011.
A farkon watan nan an kashe mutane 6 a wani hari makamancin wannan da aka kai a kan wasu baki a garin na Mandera lokacin da wasu da ake zaton ‘yan al-Shabab ne suka kai hari a unguwar.
A watan Nuwambar shekarar 2014, mayakan suka kashe mutane 28 wadanda ba musulmi ba ne, bayan da suka kame wata bus a garin na Mandera.
Haka nan a Somaliyan ma, wani dan harin kunar bakin wake da ake zargi dan al-Shabab ne, ya tada nakiyoyi da aka dankarawa wata motar dakon kaya a sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar hada kan Afirka, ya kashe akalla mutane uku. Wasu mutane biyar kuma sun jikkata.