Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya tsawaita takunkumin sayen makamai da aka sakawa Iran wanda wa’adinsa ke shirin karewa a watan Oktoba.
Yayin wata tattaunawa da kwamitin ya yi ta bidiyo a jiya Talata wacce ake yi sau biyu a shekara domin duba matsayar da aka cimma kan yarjejeniyar nukiliyar Iran da aka samar a 2015, Pompeo ya ce, “sabunta takunkumin zai tursasa hukumomin Tehran su shiga taitayinsu.
A cewar Sakataren, al’umar kasar ta Iran sun jima suna wahala suna kuma so hukumomin kasar su daidaita tafiyarsu.
A watan Mayun 2018, shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar wacce ake kira JCPOA a takaice ya kuma maido da takunkuman da Amurkan ta sakawa Iran wadanda aka janyewa su karkashin yarjejeniya.
A matsayin martani ga wannan mataki na shugaba Trump, Iran din ta fara daukan wasu jerin matakai na ganin ta cimma muradunta na bunkasa harkokin nukiliyarta.
A watan Janairu Tehran ta ce ta dauki mataki na karshe na janyewa daga yarjejeniyar tana mai cewa, ba za ta kara bin sharudan da aka gindaya mata na kayyade adadin sinadarin uranium da za ta sarrafa ba.
Facebook Forum