Bayanai na nunin cewa akwai tarin marayun dake matukar bukatar tallafi a Najeriya, ko baya ga kananan yaran da rikicin Boko Haram ya rutsa da Iyayensu a yankin Arewa Maso Gabashin kasar, akwai kuma marayun da Iyayensu suka rasa rayukan su, harma da wandan aka watsar da su sakamakon samunsu ta hanyar da bata dace ba.
A gefe guda kuma akwai yaran da Iyayensu mahaukata ne dake gararamba a titi, da suke butakar kulawa daga hukumomi da masu hali.
Shugabar kula da gidan marayu dake karamar hukumar Kwantagora, Hajiya Raliya Abdullahi, tace sukan dauki yaran ma zuwa gidajen su domin kula dasu.
Cikin wannan yanayi ne dai kwamishinan ‘yan Sandan jihar Ogun kuma dan asalin jihar Neja, Abdulmajid Aliyu, ya gina wani katafaren gidan marayu da ya lashe kudi har kimanin Naira Miliyan 40, da yace ya samu kudaden ne daga yan uwa da abokan arziki.
Yin hakan dai ya zamanto wani kalubale ga ‘yan Siyasa. Ginin marayun dai ya kunshi abubuwa da dama da suka hada da wajen wasan yara da wajen karatu harma da sashen koyon kwamfuta.
Duk da yake dai akwai kungiyoyin addinai da ke kokarin bada gudunmawa wajen taimakawa marayun a Najeriya, a daya bangaren akwai matukar bukatar da gidajen marayu na musammam domin taimakwa rayuwar bayin Allah, ta yadda rayuwarsu zata inganta.
Domin karin bayani.