Lamarin dai ya tayar da hankulan ‘yan yankin na Niger Delta, Daraktan watsa labaran rundunar Birgediya Janal Rabe Abubakar, yace sojoji na gudanar da atisaye ne a yankin domin a horar da sojojin Najeriya ta fannin yakin ruwa, ba don kaiwa yankin hari bane idan sojoji zasu kaiwa yankin hari zasuyi ne tun lokacin da tsageru ke lalata bututun Mai.
Yanzu haka dai ana tattaunawa tsakanin dattawan yankin da tsagerun Niger Delta Avengers, wanda wannan shine zaifar hara kai ga teburin sasantawa tsakanin tsagerun da gwamnatin Tarayya.
A baya ne dai dattawan yankin suka nemi ‘yan kungiyar Avengers da su dakatar da kai hare hare a yankin, lamarin da bai kawo saukin kai hare haren ba kan kamfanonin hakkar Mai da wasu sabbin kungiyoyi ke daukar alhakin kaiwa.
Domin karin bayani.