Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar DSP Jospeh Kuji ya gayawa wakilin Muryar Amurka cewa hankula sun kwanta bayan tashin hankalin.
“Yanzu kura ta lafa a Wukari babu wata damuwa, jami’an tsaro suna ko ina suna tabbatar da tsaro ga rayuwa da jama’a da kuma kayansu.” In ji DSP Kuji.
A cewar Kakakin, mutane bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da 15 suka jikkata bayan da rikici ya biyo bayan rushe zaben gwamnan jihar Darius Ishaku na jam’iyyar PDP.
A ranar Asabar din da ta gabata ne wata kotu ta rushe zaben gwamna Ishaku wanda hukumar zabe ta ayyana cewa ya lashe zaben jihar bisa dalilin cewa jam’iyyarsa ta PDP ba ta yi zaben fidda gwani ba a baya, wadan hakan ya sabawa dokar kasar.
Kotun ta kuma ba da umurnin a rantsar da 'yar takarar APC Hajiya Aisha Alhassan.
Jihar Taraba na daga cikin yankunan da ke fama da rikicin da ke da nasaba da addini da kabilanci a arewacin Najeriya inda aka yawan samun salwantar rayuka da dukiyoyi.
Saurari rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz domin jin karin bayani game da halin da ake ciki a jihar ta Taraba, saurari wannna rahoto: