Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Kano Za Ta Biya 'Yan Kasuwar Da Ta Rushe Shagunansu Naira Milyan Dubu 3


Tun farko dai ‘yan kasuwar ne suka shigar da gwamnatin Kanon a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano, suna kalubalantar matakin gwamna Abba Kabiru Yusuf na rusa musu shaguna, lamarin da suka ce ya jefa rayuwar su da ta iyalan su cikin damuwa.

Bayan shafe watanni ana shari’ar, kotun ta yanke hukunci inda ta umurci gwamnatin ta biya ‘yan kasuwar diyyar kudi naira miliyan dubu 30, bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a gaban ta.

Gwamnatin jihar Kano ta amince zata biya naira miliyan dubu uku a matsayin diyya ga ‘yan kasuwar da gwamnatin jihar Kano karkashin ikon Abba Kabir Yusuf ta rusawa kantuna a bakin harabar babban masallacin idi na Kano a makon farko da kama aiki a watan Yunin bana. Masana a fagen demokaradiyya da dokokin kasa sun fara tofa albarkacin bakin su akan lamarin.

Tun farko dai ‘yan kasuwar ne suka shigar da gwamnatin Kanon a gaban babbar kotun tarayya dake Kano, suna kalubalantar matakin gwamna Abba Kabiru Yusuf na rusa musu kantuna, lamarin da ya jefa rayuwar su da ta iyalan su cikin dimuwa. Bayan shafe watanni ana shari’ar, kotun ta yanke hukunci da ya umurci gwamnatin ta biya ‘yan kasuwar diyyar kudi naira miliyan dubu 30, bayan gamsuwa da hujjojin da aka gabatar a gaban ta.

Sai dai ganin an dauki wani lokaci gwamnatin bata ce uffan ba, ‘yan kasuwar su ka sa ke gurfanar da babban bankin Najeriya da wasu bankunan kasuwanci da gwamnantin Kano ke mu’amalar kudi dasu a gaban babbar kotun tarayya dake Abuja, domin samun wani umurni na musamman kan wadancan kudade da kotun tarayya ta ce a biya su, al’amarin daya sanya gwamnatin ta garzaya neman sulhu.

Barr. Garba Yusuf Abubakar wani lauya mai zaman kan shi a jihar Jigawa dake arewacin Najeriya, ya ce, “A irin wannan gaba, wanda ka samu hukunci akan zakayi karar wanda yake ajiye da kudin sa, kamar banki ke nan a wannan gabar, ya zo ya fadawa kotu dalilan da suka sa ba zai bayar da kudin da aka ce ya bayar ba, wadanda suke hannun shi mallakar wanda ka samu hukunci akan shi, amma hakan bai hana a yi sulhu ba, kamar yadda ta faru a wannan shari’a da gwamnatin Kano da ‘yan kasuwa”.

Yanzu dai gwamnatin jihar Kano ta yarda bisa tsarin sulhu, za ta biya wadannan ‘yan kasuwa da ke kasuwanci a gefen harabar babban masallacin di na Kano jimlar kudi naira miliyan dubu 3 saboda lalata dukiyar su da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi, kamar yadda lauyan ‘yan kasuwar Barrister Nura Ayagi ya shaidawa kotu a zaman ta na ranar 14 ga watan Disamba 2023.

Dr. Kabir Sa’idu Sufi Malamin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano ya bayyana lamarin da cewa, “ Duk inda akace anyi sulhu, an samu gamsuwa cewa, an sabawa wani, sannan kuma ake neman a samu dai-daito a Tsakani. Sai dai kuma duk lokacin da irin haka ta faru, sai ayi kokarin daukar darasi ta hanyar kiyaye afkuwar irin hakan a gaba”.

Shi kuwa Dr Sa’idu Ahamd Dukawa dake koyar da dabarun mulki da kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero Kano, cewa yayi wannan yarjejeniyar sulhun nasara ce ga bangarorin biyu.”Za’a iya cewa, wannan sulhun nasara ce ga bangarorin guda biyu, wadanda aka rusawa gidaje, watakila kudaden da aka ba su zasu iya mayar ma su da abin da sukayi hasara. Sannan kuma nasara ce ga bangaren gwamnati saboda an koyi darasi, nan gaba za’ayi takatsantsan. A bangare guda kuma, al’umar jihar Kano sun yi nasara, saboda kudi naira miliyan dubu uku, za’a iya yin ayyuka masu yawa da zasu amfani Jama’a, amma yanzu sun tafi wajen biyan diyya”.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG