Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayya Na Neman Wasu Ma’aikatan CBN Ruwa A Jallo Kan Zargin Satar Dala Miliyan $6.2m


Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

Gwamnatin tarayyar Najeriya na neman ma’aikacin CBN, Odoh Ocheme da wasu mutane biyu bisa zargin sa hannun tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na jabu na satar kudi $6.2m daga babban bankin kasar.

Gwamnatin ta bayyana haka ne a wata wasika da aka aika wa mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda ta ofishin babban mai bincike na musamman akan CBN.

Ana zargin Ocheme, tare da wani Adamu Abubakar da Imam Abubakar, da hada baki tare da rubuta takardun jabu da sunan Buhari da suka yi amfani da su wajen sace $6,230,000 daga asusun CBN.

Ma’aikatan CBN Da Gwamnati ke nema
Ma’aikatan CBN Da Gwamnati ke nema

Wasikar mai dauke da sa hannun Shugaban sashen ayyuka, ofishin mai bincike na musamman, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Eloho Okpoziakpo, ta ce:

“Mai bincike na musamman, wanda Shugaban kasa kuma babban kwamandan tarayyar Najeriya ya nada domin ya binciki CBN. Kungiyoyi da sauran manyan kungiyoyin kasuwanci na gwamnati, KGBEs, suna rokon ku da ku sanya mutane masu suna a sama akan sanarwar INTERPOL...

INTERPOL
INTERPOL

Mutanen uku da ake zargi da abokan huldar su sun yaudari CBN ta hanyar nuna cewa suna wakiltar ofishin sakataren gwamnatin tarayya.

Sun yi ikirarin cewa suna bukatar kudi ga masu sa ido kan zabe daga kasashen waje, inda suka yi awon gaba da dala miliyan 6,230.

Yanzu haka dai wadanda ake zargin ana tuhumarsu da laifuka shida a babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa laifin rashin gaskiya da suka aikata.

Wadannan tuhume-tuhumen sun nuna irin girman tuhumar da ake yi musu, kuma idan aka same su da laifi, za su fuskanci mummunan sakamako.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG