Mataimakin gwamnan jihar Taraba Haruna Manu ya jagoranci wata tawaga ta musamman zuwa yankin Mambila domin yin dubi kan irin yadda rikicin kabilanci ya kai ga asarar rayuaka da dama.
Shi dai wannan rikici da ya auku yau kusan makwanni biyu ke nan ya haddasa asarar rayuka da dama tare da jikkata wasu kana ya jefa jama’a da dama cikin halin kuncin rayuwa baya ga rayuka da dukiyar da aka rasa.
Da yake jawabi ga al’umman yankin yayin wannan ziyarar jajantawar, mataimakin gwamnan jihar Hon. Haruna Manu ya nuna takaicin gwamnatin jihar game da abun da ya jawo wannan rikici,tare da ba da tabbacin cewa gwamnatin jihar Taraban za ta tallafawa wadanda rikicin ya shafa.
Mataimakin gwamnan ya kuma kira al’ummar yankin Mambillan da su yafe wa juna domin ciyar da yankin gaba.
Kawo yanzu dai,dubban jama’a ne wannan rikicin ya raba da gidajensu inda suke samun mafaka a wajen 'yan uwa da abokanan arzika baya ga wadanda suka ketare kasar suka shiga Kamaru da kuma wadanda yanzu ke kwance a wasu asibitocin jihar.
Mata da kananan yara ne wannan rikici ya fi shafa, kamara yadda bayanai ke nunawa.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdulaziz
Facebook Forum