Biyo bayan tashin hankalin da aka samu a yankin Mambilla dake jihar Taraba inda aka samu hasarar rayuka, gwamnatin jihar ta kira wani taron masu ruwa da tsaki don gano bakin zaren da nufin sasantawa.
Wannan ne dai karon farko da Gwamnan jahar ya kira irin wannan taro na masu ruwa da tsaki na yankin Mambillan tun bayan aukuwar wannan rikici da aka shafe mako guda ana yi.
Kamar yadda wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya aiko da rahoto, a wajen wannan taro da aka gudanar a gidan gwamnati dake Jalingo, shugabanin kabilun yankin dama na Fulani da Hausawa da kuma sauran masu ruwa da tsaki duk sun bayyana takaicinsu ne bisa asarar rayukan da aka yi, inda suka zargi gwamnatin jihar da shakulatin bangaro,,zargin da gwamnan ta musanta.
Gwamnan jihar Taraban Akitet Darius Dickson Isiyaku ya tambayi daya daga cikin shugabanin al’umman Mambilan game da abun da ya jawo tashin hankalin.
Da yake bada amsa, ba tare da tsoro ba, a gaban gwamnan jihar da sauran jami’an tsaro ya fasa kwai game da rawar da wasu shugaban siyasa suka taka a wannan rikici.
Bayan kai ruwa rana da kuma musayar kalamai, gwamnan jihar ya kafa kwamitin shiga tsakani da sasantawa. To sai dai kamar sauran masu jawabi ,kwamandan soji na runduna 23 dake Yola, da kwamishinan yan sandan jihar da sauran shugabanin tsaro a jihar Taraban, duk sun aza laifin ne ka abun da suka kira wariya, da son kai da kuma bangaranci, wanda suka ce muddin ana son cin nasara to fa labudda sai an magance wadannan matsaloli.
Facebook Forum