Gwamnatin Nigeria ta ce tana ci gaba da nemo hanyoyn shawo kan matsalar da ta addabi wutar lantarki a kasar.
A wani babban taron masu ruwa da tsaki a harkokin wutar lantarki, Ministan Makamashi da Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola ya ce taron na Minna zai maida hankali ne akan matsalolin da suke kawo cikas a harkokin wutar lantarki.
Ministan y ace ana fuskantar matasloli biyu ne, samun mitoci ga masu anfani da ita da kuma raba wutar. Ya yi imanin cewa a taron zasu ji bahasinsu daga bakin masu ruwa da tsaki a kan harkokin wutar lantarkin.
Kwamishanan ayyuka na jihar Niger Alhaji Ibrahim Balarabe wanda ya halarci taron ya ce taron yana da anfani matuka a daidai wannan lokacin. Alhaji Balarabe y ace akwai wuta amma masu raba ta suna da matsalar ingantattun kayan aiki irin na zamani. Kalubalen dake fuskantarsu ke nan har sai sun samu kayan aikin da suka dace.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari
Facebook Forum