Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan sanda Sun Ce Sun Cafke Gungun Barayin Da Suka Kashe Farfesa Halima Idris.


Babban Sifeton 'Yan Sandan Nigeria Ibrahim Idris
Babban Sifeton 'Yan Sandan Nigeria Ibrahim Idris

Yayin da 'yan sandan Nigeria suka bada sanarwar cafke gungun 'yan bindigan da suka kashe Farfesa Halima Sa'adiya Idris tsohuwar kwamishaniyar ilimi a jihar Katsina akan hanyar Kaduna zuwa Abuja, wani mai sharhi akan lamuran 'yan sandan na fatan sanarwar sahihiya ce.

Kakakin rundunar 'yan sandan Nigeria, Jimoh Moshood, ya sanar da cafke gungun barayin da suka kashe mutane akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, da suka hada da Farfesa Halima Sa'adiya Idris, tsohuwar kwamishaniyar ilimi ta jihar Katsina.

Cikin wadanda aka kara cafke wa har da 'yan fashi da makamin da suka afka gidan daraktan cibiyar binciken ayyukan gona ta Jami'ar Ahmadu Bello, Farfesa Kalib Uthman, inda suka yi garkuwa da wata mata mai jego tare da jaririnta.

Speto Janar na 'yan sandan Nigeria Alhaji Ibrahim Idris, ya kuma umurci duk 'yan sandan kwantar da tarzoma dake jihar Kaduna da yanzu suke waje su gaggauta su koma Kadunan domin samar da cikakken tsaro a jihar.

Shuaibu Mungadi wani mai sharhi akan alamuran 'yan sanda a Nigeria, ya ce idan mutanen da aka kama su ne suka aikata laifin to ana iya cewa 'yan sandan sun cancanci yabo. Idan kuma rashin kayan aiki ne ya sa sai an aikata laifi suke yunkura to ya kamata a samar masu da isassun kayan aiki.

A cewar Mungadi ana zarge zarge da yawa akan ayyukan 'yan sanda a kasar saboda sau tari su kan kama mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a dora masu laifi da zummar samun yabo daga al'umma ko kuma su fitar da kansu daga zargin gwamnati.

Akwai zargin cewa 'yan sandan nada bata gari da yawa a cikinsu dake aikata miyagun ayyukan dake faruwa. An sha samun bata garin amma ba'a jin matakin da hukumar 'yan sandan take dauka a kansu.

A saurari rahoton Hassan Maina Kaina

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:13 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG