Jami'an guda biyar ana zarginsu da wawure kudin gwamnati N2.9b a lokacin da suke mulki a karkashin gwamna Babangida Aliyu.
Tsoffin jami'an da aka cafke sun hada da manyan sakatarori guda uku da tsohon shugaban ma'aikata na gidan gwamnatin jihar da kuma wani tsohon shugaban karamar hukuma.
Kwamishanan 'yansandan jihar Alhaji Abubakar Marafa yace wani kwamitin siri ne da gwamnatin jihar ta kafa domin bankado kudaden da aka kashe ba akan kaida ba ya tono badakalar. Kwamitin ya kunshi 'yansanda da SSS da jami'an gwamnatin jihar.
Kawo yanzu kakakin gwamnan jihar Jibril Baba Ndache yace ko bayan guda biyar din da aka cafke akwai wasu da dama da suke bincike. Ndache yace ana cigaba da bincike kuma ana kiransu a yi masu tambayoyi kuma duk inda aka tabbatar an yi ba daidai ba dole a kwato kudaden a yiwa jama'a aiki dasu.
Wadanda suka amsa laifin sun soma dawo da kudaden da suka handame. To amma har yanzu tsohon gwamnan jihar Babangida Aliyu bai ce komi ba akan batun. To saidai Alhaji Muhammad Sani na hannun daman tsohon gwamnan yace lamarin bita da kuli ne kawai irin na siyasa.
Ga karin bayani.