Tun a ranar 6 ga watan nan na Afrilu ne dai kungiyar ta tsunduma yajin aiki, domin nuna adawa da yadda aka ki aiwatar da ‘yancin cin gashin kan bangaren shari’a.
Ministan Kwadago Chris Ngige ya jagoranci wani zaman sulhu tsakanin gwamnatin tarayya da shugabancin kungiyar a Abuja, inda ya roke su da su dan kara hakuri da ba da lokaci.
Ngige ya tunatar da su cewa suna cikin “ma’aikatan da aka fi bukata a kullum kamar likitoci, don haka bai kamata su shiga yajin aiki ba.”
Ministan ya ce ba yadda za’a yi Najeriya ta yi wani abin ci gaba ta bangaren tattalin arziki, alhali babu ma’aikatan da ke tabbatar da bin doka da oda.
“Ku muhimman mutane ne, wannan ya sa muka jira mu ga ko za mu iya samun sulhu na cikin gida tare da alkalin-alkalai na kasa” in ji Ministan Kwadago Chris Ngige, “amma tunda ba’a sami nasara ba, hakan ya sa muga gwada na mu hakkin a nan ma’aikatar kwadago ta tarayya.”
Ministan ya ba su tabbacin cewa za’a magance korafinsu na aiwatar da tsarin ‘yancin cin gashin kai na bangaren shari’a.
Karin bayani akan: Ministan Kwadago Chris Ngige, Yajin Aiki, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
“A nan ma zan ba ku tabbacin cewa dokar nan ta 10 da tanade-tanadenta da suka baiwa bangaren shari’a ‘yancin cin gashin kan sa, wanda shi ne babbar bukatarku, zai tabbata, saboda sha’ani ne na kundin tsarin mulki.”
A martanin da ya mayar, shugaban kungiyar ma’aikatan shari’a na kasa Marwan Adamu, ya ce an kafa kungiyar ne da dukkan ayukanta bisa tafarkin tsarin mulki, yana mai cewa ita kuwa dimokaradiyya tana wanzuwa ne kawai tare da bin doka da oda.
Adamu ya ci gaba da cewa “ita ma Najeriya kasa ce da kundin tsarin mulki ya gina ta, amma kuma mun lura ba’a bin wasu tanade-tanaden tsarin mulki, kamar wanda ya baiwa bangaren shari’a ‘yancin cin gashin kan sa.”