Biyo bayan harin da mayakan Boko Haram suka kai garin Garkida dake arewacin jihar Adamawa, a karon farko gwamnatin tarayyar Najeriya ta tura wasu kayayyakin tallafi na abinci garin a daidai lokacin da al’ummar yankin ke kira da a duba halin da suke ciki.
Sakamakon harin mayakan sun lalata dukiyoyin jama’a da gine-gine da suka hada da asibiti, majami’u da gidaje bayan asarar rayukan da aka yi.
Mr. Andrawus Terfa, tsohon shugaban kungiyar ‘yan jaridar NUJ reshen jihar Adamawa, ya ce cikin gidajen da aka kona har da na talakawa kuma sake gina wani gidan na da wahala a yanayin da ake ciki.
Kayayyakin tallafin da gwamnatin kasar ta turawa wadanda harin ya shafa sun hada da shinkafa da turamen zannuwa, da kuma tabarmi.
Hajiya Sadiya Farouq, Ministar harkokin jinkai ta Najeriya, ta ce sun kai wannan ziyarar ne bisa umurnin shugaba Muhammadu Buhari don jajantawa al’ummar jihar da gwamnatinsu da kuma duba yadda za a kara taimakawa wadanda suka rasa matsugunnansu.
Sakataren hukumar kai dauki ta jihar da ake kira ADSEMA, Muhammad Aminu Suleiman ya tabbatar da cewa hukumomin bada agaji a jihar sun fara kai kayayyakin ga wadanda abun ya shafa kuma ana sa ido sosai.
A ‘yan kwanakin nan dai an samu sabbin hare haren ‘yan Boko Haram a jihohin Adamawa, Borno da kuma jihar Yobe, batun da shugabannin addini ke ganin dole ne hukumomi su tashi tsaye wajen kare rayukan al’umma. Sheikh Abdullahi Bala Lau shine shugaban kungiyar Izala a Najeriya, ya jaddada bukatar hukumomi su tashi tsaye wajen kare jama’a saboda ta’addanci ba shi da addini.
Shi ma shugaban kungiyar kristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Adamawa, Rabaran Stephen Dami Mamza ya ce har yanzu akwai matsalar tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya kuma gwamnati ba ta fadin gaskiyar halin da ake ciki game da batun ‘yan Boko Haram.
Ga karin bayani cikin sauti.