WASHINGTON DC —
Wannan makon shirin Kallabi zai haska fitila kan hatsarin tura kananan yara Mata talla da ake yi a kasashen da dama. Alkaluma na nuni da cewa sama kananan yara Mata miliyan 65 ne a fadin duniya basa zuwa makaranta, yayinda da dama daga cikin wadanda ke zuwa makarantar kuma basa yin nisa a karatu bisa dalilai daban daban.
Sannan Shirin zai kamala tattaunawa da Mama Sarah Jibril, mace ta farko da ta taba tsayawa takarar shugaban kasa a arewacin Najeriya.
Saurari cikakken shirin cikin sauti:
Dandalin Mu Tattauna