Gwamnan jihar Aminu Bello Masari, ya kuma yi alkawarin taimakawa jami’an tsaro wajen yin rajistar duk makaman da wasu nagartattun mazauna jihar suka samu ba bisa ka’ida ba.
"Za mu goyi bayan wadanda suka zo da shirin sayo makamai saboda mazauna yankin na bukatar su kara kaimi ga kokarin hukumomin tsaro. Abin mamaki ne yadda dan fashi zai mallaki bindiga alhali mutumin kirki na kokarin kare kansa da iyalansa ba shi da ita,” Masari ya ce kamar yadda rahotanni suka ruwaito.
Da yake jawabi yayin ganawa da manema labarai a gidan gwamnati da ke Katsina a ranar Talata, gwamnan ya kuma bukaci jama’a da su marawa kokarin jami’an tsaro na samar da tsaro a cikin al’umma.
Gwamna Masari ya kuma kara da cewa; Musulunci ya halatta mutum ya kare kansa daga hari. Dole ne mutum ya tashi ya kare kansa, danginsa da dukiyoyinsa. Idan ka mutu kana kokarin kare kanka, za a dauke ka a matsayin shahidi.''
Ya kuma jaddadda cewa Najeriya ba ta da isassun ‘yan sanda da sojoji da za su kare rayuka.
Kalaman na Masari na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni daga fadar shugaban kasa suka nuna cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarnin a dauki karin 'yan sanda 10,000 a sassan kasar.