Gwamnatin jihar ta bayyana hakan ne a yayin wata hira da manema labarai da kwamishinan yada labaran jihar, Malam Sanusi Sa’id Kiru, ya yi a jihar Kano a ranar Alhamis inda ya sanar da matakin da gwamnatin ta dauka.
Sanusi Sa’id Kiru ya kara da cewa gwamnati ta bullo da wannan matakin ne domin a samu kafar tattara cikakkun bayanan daliban da ke makarantu a fadin Jihar saboda gwamnati ta sami sauki wajen inganta yanayin tsare-tsarenta, ayukan kasafin kudi da kuma rage aikata ba daidai ba a duk lokacin jarrabawa.
Mallam Kiru ya kuma ce shirin yin rijista ga daliban makarantun sakandaren zai taimakawa ma’aikatar yada labaran jihar ta kara samun sahihan bayanai ta hanyar daukar zanen yatsu guda goma wato 'fingerprint' da kuma fasfo wato hoton fuska tare da sa hannun kowanne dalibin jihar a kundin bayanai daya.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga hukumar da ke Kula da manyan makarantun sakandare ta Jihar wato KSSSMB da cibiyoyin kula da ayukan ilimi a jihar na shiyya-shiyya, da shugabannin makarantu da daraktoci da su sa ido domin tabbatar da cewa an aiwatar da umarnin gwamnatin jihar yadda ya kamata domin a samu ci gaba.
Kiru ya bayyana yadda ma’aikatar yadda labarai da ya ke jagoranta ta kammala shiri da ofishin hukumar kula da aikin yin rijistar shaidar zama dan kasa a Jihar, domin nemawa daliban sauki wajen mallakar lambar a matakin shiyya-shiyya a maimakon yin dogon tafiye-tafiye.
Da muka tuntubi kwamishinan yadda kabaran jihar ta wayar tarho don karin bayani ba mu same shi ba saidai wakilinmu a jihar Kano na bin diddigi kan lamarin don kawo karin bayani kan aikin samun lambar NIN ga daliban.