Gwamnatin kasar ta dauki wannan matakin ne sanadiyar gasar kwallon kafa na mata na kasashen Afirka da kasar ta dauki bakuncinsa.
Dangane da wannan sabuwar dokar wani direba mai sana'air aikin taksi yace dokar bata yi masu dadi ba saboda ba'a yi masu wani tanadi ba. Yace wadansu daga cikinsu basu da komi sai tsoffin motocinsu. Amma idan gwamnati zata taimaka masu da kafa masu bankunan da zasu basu lamunin sayen sabbin motoci zai yi kyau. Idan ba haka ba yawancinsu zasu shiga cikin halin kakanikayi.
Yace idan mutane suka rasa aiki suna iya zama barayi saboda yawan iyalai.Wani Alhaji Danjuma Adamu mai ba gwamnati shawara a bangaren lamuran sufuri yace a Kamaru mutum daya nada motoci goma, ishirin ko fiye da haka ana yi masa aiki dasu. Yace dangane da tsoffin motoci dole ne a dauki mataki domin bakin da zasu zo. Yace wasu motocin basu dace su dinga yawo a hanya ba.
Yace dama can duk motar da aka ce taksi ce to sai tana da lafiya ake bari ta yi tafiya a hanya. Yace duk wanda ya dace ita ma gwamnati zata duba ta gani. Amma shawarar samun motoci da suke da inganci a hanya mataki ne mai kyau.
Barrister Haruna Yakubu yayi tsokaci akan abun da gwamnatin Kamaru zata yi domin ba direbobin hakkinsu idan har an hanasu aiki da tsoffin motoci. Yace bisa dokar kasa da ya gani bai ga abun da zai hana dan kasa yin aikinsa ba. Idan gwamnati tana son hanasu aiki da tsoffin motoci to ta samar masu abun da zasu yi kamar basu tallafi. Yace kada a manta akwai kungiyar 'yan ta'ada ta Boko Haram kuma idan mutane basu da aikin yi ta'adanci na iya karuwa.
Ga karin bayani.