WASHINGTON, DC - Gwamnatin jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya ta sanar da bai wa al'umar jihar izinin mallakar makamai don kare kansu daga hare-haren 'yan ta'adda.
kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Ayuba Elkana ya ce har yanzu dokar hana bada lasisin mallakar bindiga na aiki. Ya kara da cewa rundunar ta daina ba 'yan kasa lasisin mallakar bindiga, a cewar kafar yada labaran Punch ta Najeriya.
A wata hira da Muryar Amurka, Kwamishinan yada labaran jihar Zamfara Ibrahim Dosara, ya tabbatar da cewa gwamnatin ta ba al’umar jihar damar mallakar makamai duba da yadda ‘yan ta’adda ke kara kai hare-hare kan al’uma.
Dosara ya ce gwamnati ta damu ainun saboda dawowar kai hare-haren ‘yan bindiga a sassan jihar Zamfara da a baya suka lafa kuma la’akari da yanayin damina da ake ciki yanzu ya sa gwamnatin ta ga ya kamata manoma su kare kansu.
Ya kara da cewa gwamnati zata taimaka wa mutane su samu lasisin mallakar makamai daga babban Sufeton 'yan sandan Najeriya ta hanyar kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara bayan tabbatar da cancantar wanda zai mallaki makamin.
Dosara ya kuma ce gwamnati ta kafa wani kwamiti da zai karbi rahotanni a kan masu ba 'yan ta’adda bayanan sirri don su kai hari kan al'uma. A saboda haka gwamanati ta umurci majalisar dokokin jihar da ta gaggauta aiwatar da dokar da aka yi kan masu ba 'yan ta’adda bayanai don cutar da al'uma.
Gwamnatin jihar ta kuma yanke shawarar kara yawan mutane a masarautun jihar da zasu yi aikin tsaron al’uma daga 300 zuwa 500, a cewar Dosara.
Saurari hirar Sani Shu'aibu Malumfashi da Dosara: