Tun kimanin watanni 2 da suka gabata kenan dai da kasa ta rufe wadansu masu hakar ma'adanai a yankin na Galadiman ogo ta karamar hukumar Rafi, da kawo yanzu aak lalubo gawarwakin mutane 10 sannan aka samu 8 da ransu inda har ya zuwa yanzu ake ci gaba da kokarin zakulu gawarwakin wasu mutane 4.
Sakataren gwamnatin jihar Nejan Alhaji Abubakar Usman yace duk da yake kamfanin dake aiki a wannan wuri ya sabawa ka'ida, gwamnati ta nuna jinkai ne shi yasa ta tausayawa iyalan wadanda lamarin ya shafa.
A yanzu dai An kafa wani kwamiti da aka baiwa mako biyu domin aikin tantance iyalan wadannan mutane,
Alh.Umar Aliyu Bala Shine Hakimin yankin na Galadiman Kogo tun daga lokacin da lamarin ya faru babu wani tallafi da suka samu daga gwamnati sai yanzu, yayinda ake ci gaba da bincike domin gano wadanda har yanzu suke cikin ramin.
Gwamnatin jihar Nejan dai tace har yanzu dokar hana hakar ma,adanan kar kashin kasa ba akan ka'idaba tana aiki daram al'amarin da tace yana daya daga cikin matakan da take dauka domin shawo kan matsalar rashin tsaro da ya addabi wasu yankuna na jihar.
saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna