Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Anambra Ta Yi Tur Da Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Ayarin Motocin Ofishin Jakadancin Amurka


Rundunar yan sanda
Rundunar yan sanda

Gwamnatin jihar Anambra ta bayyana bacin ranta tare da yin Allah wadai da harin da wasu ‘yan bindiga suka kai kan wani ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka, wanda ya yi sanadin mutuwar jami’an ofishin jakadancin guda biyu da ‘yan sanda biyu a yankin Ogbaru na jihar a yammacin ranar Talata.

Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta kuma bayyana cewa maharan sun cinna wa gawarwakin jami’an da motocinsu wuta.

“Gwamnatin jihar Anambra ta yi bakin cikin aukuwar wannan al’amari mai ban takaici, wanda ke zuwa a lokacin da jihar ta fara ganin ci gaba a fannin tsaro," a cewar Mr. Christian Aburime, kakakin gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar ta kuma yi Allah wadai da wannan harin kuma ta sha alwashin zakulo duk wadanda suka aikata wannan ta’asar a duk inda suka boye.”

Harin da yan bindiga suka kai
Harin da yan bindiga suka kai

Ya zuwa yanzu dai ba a kama maharan ba, amma ‘yan sanda sun ce suna ci gaba da gudanar da bincike da farautarsu a karamar hukumar Ogbaru inda harin ya auku.

“Aiki na ci gaba da gudana. An kaddamar da bincike a garin Ogbaru,” a cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tochukwu Ikenga. Ya kuma ce zasu bada karin bayani nan gaba.

Tuni dai Fadar White House ta Amurka ta bayyana cewa ma’aikatan ofishin jakadancin nata ‘yan Najeriya ne harin ya rutsa da su, amma babu wani Ba’amurke a cikinsu.

Karamar hukumar Ogbaru na kara kaurin suna a jihar Anambra da ke fama da ayyukan ‘yan bindiga, don ko a watan Afrilun bara wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ofishin ‘yan sanda a garin Atani da ke karamar hukumar, inda suka hallaka ma’aikata hudu.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG