Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Gbagbo ta nuna alamar bijirewa kwamitin Kungiyar Hadin Kan kasashen Afrika


Firai Ministan kasar Kenya Raila Odinga a wata hira da manema labarai kan batun Ivory Coast
Firai Ministan kasar Kenya Raila Odinga a wata hira da manema labarai kan batun Ivory Coast

Gwamnatin kasar Ivory Coast ta shugaba Laurent Gbagbo mai ci yanzu, tace zata yi watsi da duk wani binciken da zai nuna cewa Mr. Gbagbo ya fadi zaben shugaban kasar

Gwamnatin kasar Ivory Coast ta shugaba Laurent Gbagbo mai ci yanzu, tace zata yi watsi da duk wani binciken da zai nuna cewa Mr. Gbagbo ya fadi zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba wanda ake takaddama a kai. Ministan harkokin kasahen ketare na Mr. Gbagbo Alcide Djedje, ne ya bayyana haka ga manema labarai kwana daya bayanda Kungiyar Tarayyar Africa ta sanar da sunayen shugabannin da zasu yi kokarin warware rudamin siyasar kasar Ivory Coast. Djedje yace shugabannin suna iya ziyartar Ivory Coast amma gwamnatin Gbagbo ba zata amince da sakamakon bincikensu ba muddar ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Majalisar tsarin mulkin kasar Ivory Coast tace Mr. Gbagbo ne ya lashe zaben da aka gudanar a watan Nuwamba bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da abokin hamayyarsa, Alassane Quattara a matsayin wanda ya lashe zabe. Kungiyar Tarayyar Afica da Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyar hadin kan tattalin arzikin Afrika ECOWAS duka sun ce Mr. Quattara ne ya lashe zaben.

XS
SM
MD
LG