WASHINGTON, D.C - Deby ya ayyana kansa a matsayin shugaban majalisar soji ta rikon kwarya a watan Afrilun 2021 bayan an kashe mahaifinsa Idriss Deby, wanda ya dade yana mulki, yayin da ya ziyarci sojojin da ke yaki da ‘yan tawaye a arewa.
Da farko majalisar ta ce za ta sa ido kan mika mulki na tsawon watanni 18 zuwa mulkin dimokradiyya, amma ba ta nuna alamar shirya zabe ba yayin da wa'adin ke karatowa.
Deby ya gabatar da tattaunawar kasa a matsayin matakin farko na shirya kada kuri'a.
An fara samun matsin lamba daga kungiyoyin adawa na kasar Chadi da abokan huldar kasar don ci gaba da tsarin mika mulki. Kasar Chadi kawa ce ga Faransa da sauran kasashen yammacin duniya a yakin da ake yi da masu kaifin kishin Islama a yankin Sahel na Afirka.
-Reuters