Saboda samun sahihin gaskiyar maganar Muryar Amurka ta zanta da kakakin shugaban kasar Najeriya Malam Garba Shehu.
Yace ba gwamnatin Najeriya ce ba zata nadawa Boko Haram kungiyoyin da zasu wakilceta a tattaunawa da ita akan warware batun 'yan matan Chibok. Yace abun da Shugaba Buhari yake cewa shi ne idan har 'yan Boko Haram basu amince su fito su zauna da wakilan gwamnati a teburin shawara ba, suna iya biyowa ta hannun wasu kungiyoyi da suka amince dasu.
Garba Shehu yace akwai kungiyoyi da yawa kamar su Red Cross, Red Crescent da ma wasu kungiyoyin addini dake kasashen waje da kan bada gudummawa akan irin alamura masu kama da abun dake faruwa tsakanin gwamnati da 'yan Boko Haram.
Amma gwamnati na bukatar ta tabbatar cewa 'yan matan suna hannunsu. Abu na biyu shi ne su 'yan Boko Haram su lissafa sunayen wadanda suke so a sako masu.
Dangane da cewa ya kamata gwamnati ta gayawa iyayen cewa watakila ba za'a samu 'yan matan kamar yadda suke da ba, sai Garba Shehu yace ai gwamnati bata san yadda suke ba saboda haka ba zata yaudari iyayen ba. Yace wasu kungiyoyin dake fafutikar a sako 'yan matan suke yaudarar iyayen.
Malam Garba Shehu yace yarinyar da ta fito da diya ta fada cewa an bazasu ta dalilin aure.
Ga tattaunawar da Muryar Amurka tayi domin karin bayani.