Muryar Amurka ta yiwa kakakin shugaban kasar Najeriya tambaya akan abun da shi Shugaba Buhari ya rubuta a yanar gizo ta kafar tweeter akan 'yan matan da Boko Haram.
Da aka tambayi Garba Shehu kakakin shugaba Buhari abunda yake nufi da abun da ya rubuta sai yace "Shugaban kasa yana nuna cewa ba tare da gindiya wasu ka'idoji ba ashirye gwamnatinsa take ta tattauna da duk wani wanda yake an hakikance yana da karbuwa a cikin kungiyar kuma suna da 'yan matan a hannunsu"
Ya cigaba da cewa abun da shugaban yake nunawa shi ne shi bai ajiye wasu sharruda ba akan yin magana da 'yan Boko Haram ko kuma musayar 'yanuwansu da ake rike dasu domin su sako 'yan matan Chibok. Abun da zai kwantarwa shugaban hankali shi ne a dawo da 'yan matan.
Dangane da fargaban cewa idan aka yi musaya da 'yan ta'addan watakila nan gaba wasu kungiyoyi ka iya fitowa su ma su aikata irin ta'asar 'yan Boko Haram domin su samu fansa. Sai Garba Shehu yace su fito mana domin kowa ya san Shugaba Muhammad Buhari kuma ashirye yake.
Yace yin musaya da firsinoni kasar Israila tayi. Amurka ma tayi saboda haka ba sabon abu ba ne a tsarin gudanar da mulki a duniya.
Sai dai masana harkokin tsaro na jan hankalin gwamnati da tayi takatsantsan kamar irinsu Air Commodor Ahmed Tijjani Baba Gamawa.Yace an sha yin magana da 'yan kungiyar amma da zara an zo a zauna teburin shawara sai su ce basu yadda da mutumin da yayi magana da yawunsu ba. Yace mutanen basu da amana. Yace zasu zo su yaudari mutane kana su cigaba da yin abubuwan da su keyi.
Shi ma Malam Gimba Ahmed na jaridar Leadershi cewa yayi tattaunawa ko sassauci da 'yan ta'ada babu abun da zai tsinana sai kara ta'addanci.
Ga rahoton Hssan Maina Kaina da karin bayani