A taron da yayi da majalisar limaman Abuja a fadarsa yau Alhamis, shugaban ya bukaci lamaman addini da su dinga kwantar da hankulan jama’arsu a duk fadin kasar. Yace shugabancin kasar, a mataki daban daban, na kokarin warware matsalolin talauci da rashin aikin yi da na tsaro da suka addabi kasar.
Yace gwamnati ta ba aikin noma fifiko domin kirkiro ayyukan yi ma miliyoyin ‘yan kasar da kuma ba kasar damar ciyar da kanta ba tare da tsoron yunwa ba. Kodayake an soma kokari gadan gadan akwai babban shirin samarda taki da maganin kashe kwari da kuma shiri ma daminar badi.
Domin kowa ya ci muradun wannan shirin shugaban yace an bukaci gwamnatocin jihohi da shugabannin al’umma, a duk fadin kasar, su yi kungiyoyin hadin kai na taimakan juna ko cooperatives tare da nanata cewa taimako irin na dabaru da kayan aiki za’a ba mutane ba kudi ba.
Shugaban ya kuma shaidawa shugabannin addinin kokarin da gwamnatinsa keyi domin inganta wutar lantarki a kasar. Saboda haka ne ma kasar zata kawo wadanda zasu saka jari a harkokin wutar lantarki daga kasar Sin da wasu kasashen da kasar ke abokantaka dasu da suke son saka jari a aikin wuta da za’a yi a Mambila da wasu wuraren.
Buhari ya tabbatar cewa matakan da gwamnatinsa take dauka a kan rikicin yankin Niger Delta zasu kaiga dawamammen zaman lafiya.
Dangane da yakin da ya keyi da cin hanci da rashawa da ‘yan ta’adan Boko Haram, Shugaba Buhari yace gwamnatinsa zata dage, babu gudu babu ja da baya. “Bamu da niyyar tursasawa kowa ko cin mutuncin wani. Adalci da tabbatar da yakamata da ba kowa hakkinsa muka sa a gaba, inji Shugaba Buhari.
Ya sake jaddada cewa duk wanda aka samu ya saci kudin jama’a to za’a tilasta masa ya dawo dasu domin kasar na bukatar kudin.
Tun farko, a madadin sauran limaman, shugaban majalisar limaman dakeAbuja Dr Tajudeen Muhammad Bello Adigun ya yaba da mulkin Buhari musamman yaki da cin hanci da rashawa da ‘yan Boko Haram. Kana ya jawo hankalin shugaban kan tattalin arzikin kasar, da matsalar kiwon lafiya da Rashin aikin yi.