Yau shekara goma sha shida ke nan da fara aikin amma ba'a kammala ba sai da gwamnatin shugaba Muhammad Buhari ta kama aiki ta kammalashi kana ta kaddamar dashi yau domin ya fara aiki gadan gadan.
Shugaban majalisar dattawa Dr. Bukola Saraki da takwaransa na majalisar wakilai Yakubu Dogara sun kasance a wurin kaddamar da layin. Haka ma akwai ministoci da gwamnoni da manyan ma'aikatan gwamnati da 'yan kasuwa.
Yayinda yake kaddamar da layin shugaba Buhari ya jinjinawa gwamnatinsa da kamfanin da ya gina layin. Yace abun farin ciki ne ganin yadda aka kaddamar dashi bayan shekaru 16 da fara aikin.
Shugaban yace layin zai taimakawa mutane wurin yin bulaguro daga Abuja zuwa Kaduna kana ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa gwamnatinsa zata ciga da daukan irin wannan matakin na habaka harkokin sufuri da zai habaka muamalar cinikayya da kasuwanci tsakanin bangarori daban daban na kasar.
Da yake nashi jawabin Dr. Bukola Saraki yace babu kasar da ta cigaba ba tare da habaka harkokin sufuri ba ta yadda kowa na iya tafiya inda yake so ba tare da wata matsala ba. Kasashe ashirin da suka habaka tattalin arzikinsu sun dogara ne akan layin dogo wurin aikewa da kaya da sakwanni da jigilar mutane.
Ga karin bayani.