Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya ce hanyar Maiduguri zuwa Bama ta gwamnatin tarayya ce, amma gwamnatinsa za ta sake shimfida hanyar domin dakile matsalar tsaro tare da tamakawa al’umomin dake amfani da ita.
Ita dai hanyar an shimfida ta ne tun shekarar 1964 ta na da tazarar kilomita 65 daga garin Maiduguri. Yanzu haka dai an saka wa’adin kwanaki 915 a matsayin kwanakin da za a kammala aikin hanyar.
Gwamna Zulum, ya ce an kebe Naira Biliyan biyar domin fara wannan aiki, ta karkashin ma’aikatar ayyuka ta MCRP. Kwamishinan ma’aikatar sake gine-gine da tsugunnar da jama’a, Kwamrad Mustapha Gubio, ya ce ganin cewa babbar hanya ce da ta dangana har zuwa Afirka ta Tsakiya da Sudan da kuma Kamaru, da zarar an kammala ta za a samu ci gaban tsaro da kasuwanci.
Rashin kyawun hanyoyi na daga cikin manyan matsaloli da ake fuskanta a jihar Borno, musamman manyan hanyoyi da suka hada jiha da jiha da kuma kasa da kasa, wanda masu aikata laifuka ke amfani da shi wajen farma matafiya.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Haruna Dauda.