Gwamnan jihar Bala Abdulkadir Muhammed ya tabbatar da hakan a jakabin da ya gabatarwa al’ummar jihar, sai dai ya musanta cewa mace-macen na da alaka da cutar coronavirus, inda ya ce mutum guda ne aka tabbatar cewa cutar ta COVID-19 ce ta yi ajalinsa.
Ya ce a cikin wadanda suka mutu akwai masu cutar hawan jini, akwai mata da suka mutu wajen haihuwa da dai sauransu.
A halin da ake ciki, gwamnan na jihar Bauchi ya ayyana dokar kulle ta tsawon kwanaki goma a yankunan kananan hukumomi uku da ke iya kasancewa kafafe na shigo da curar coronavirus a jihar, kasancewar suna makwbtaka da jihohin Jigawa da Kano.
Kananan hukumomin sun hada da Katagun, Giade da kuma Zaki, inda ya umurci mataimakinsa Sanata Baba Tela da ya ya koma yankin arewacin jihar domin tabbatar da cewa an kafa kwamitoci don shawo kan matsalar.
Wani mazaunin garin Azare ya yi wa wakilin muryar Amurka bayani akan batun mace-macen, da kuma bukatar da ke akwai ta kawo dauki ga jama’a.
Saurari karin bayani cikin sauti daga Abdulwahab Muhammad.
Facebook Forum