Wasu ‘yan bindiga sun kai hare hare a kauyuka biyar a Karamar Hukumar Batsari ta Jahar Katsina, inda su ka yi awon gaba da dabbobi da yawa baya sauran sace-sacen da su ka yi a kauyukan bayan kisan da su ka yi.
Wani ganau ya ce mutanen kauyukan sun gudu sun shiga daji wasu kuma sun hau kan duwatsu. Don haka ba a san adadin mace-mace ba har sai a gama dawowa. Da amma ya ce daga bisani, bayan da ‘yan bindigar su ka gama aika-aikarsu, sun ga wani jirgin yaki ya gitta ta wurin.
Kwamishinan ‘yan sandan Jahar Katsina, CP Sanusi Buba, wanda aka tuntube shi game da wannan al’amari, ya yi kira ga jama’a da su bada hadin kai ga ‘yan sanda. Ya yi zargin cewa akwai masu yi wa harkar tsaro zagon kasa, wanda ya ce ba zai amfani kowa ba.
Shi kuwa wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum wanda aka sakaya sunansa, ya yi kiran da a shiga yin addu’o’i tare da ba da jami’an tsaro kwararan bayanai sannan kuma a yi dirar mikiya ma irin wadanndan wuraren dare kuma da kakkafa sansanonin sojin da za su iya kau dauki cikin gaggawa. Ya ce babbar matsalar ita ce muddun su ka ji sunan mutum na bayani sai su nemi shi su kasha. Ya ce ya kamata gwamnati ta kara himma duk da yake an san ta na kokarinta.
Ga Sani Malumfashi da cikakken rahoton:
Facebook Forum