Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Amurka Ta Gargadi Amurka Su Kauracewa Kwango Kinshasha


John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka
John Kerry sakataren harkokin wajen Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka, ta fitar da wata sanarwar gargadi ga ‘yan kasarta, kan Jamhuriyar Dimokradiyar Congo, inda ta umurci iyalai da ma’aikatan gwamnatin Amurka da ke kasar da su fice.

Wannan sanarwar gargadin, ta yi nuni da cewa akwai yuwuwar barkewar rikici a wasu yankunan Kinshasa da sauran manyan biranen kasar.

Rikici dai ya barke a kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ne, saboda aniyar shugaba Jospeh Kabila ta ci gaba da zama a kan karagar mulki.

Daga ranar 19 ga watan Disamba ne wa’adin Kabila zai kawo karshe, wanda hakan ke nufin zai kammala wa’adinsa na biyu ke nan kamar yadda doka ta tanada masa, domin kundin tsarin mulkin kasar bai amince da yin wa’adin na uku ba.

Sai dai hukumar zaben kasar ta ce ba za ta iya gudanar da zabe ba har sai a karshen shekarar 2018.

Shi dai Shugaba Kabila bai ce komai dangane da haka ba, amma masu lura da al’amura sun ce yana yunkuri ne ya ci gaba da zama akan karagar mulki, lamarin da ke haifar da mummunar zanga zanga a kasar,wacce ke tsakiyar Afrika.

XS
SM
MD
LG