Gwamnan Kano yace sun fadawa wakilan arewa a taron kasa kada su bari a cuci yankin arewacin kasa. Kana an fada masu su dago batun batun man fetur da ake hakowa a cikin jihar da wanda ake hakowa a kan taekun ruwa.
A wurin taron gwamnan yayi korafin cewa babu wanda yayi maganar man da ake hakowa cikin jiha da na teku. Abun da aka yi magana a kai shi yadda za'a karawa wasu kason kudi dari bisa dari da dai sauransu. Yace arewa ma da ta nemi kaso dari bisa dari daga kudin man da ake hakowa cikin teku sabili da halin da arewa ke ciki. Akwai kwararowar hamada da wasu matsaloli da sai a rago kudinsu a kawowa arewa. Wannan shi ne yakamata a ce abun da wakilan suka maida hankali akai ke nan.
Ko menene 'yan Niger Delta suka nema ba ita ce magana ba. Abun da yakamata a yi musamman domin kare muradun arewa ita ce magana. Abun da a keyi yanzu, inji gwamnan dauke hankalin jama'a ne kuma bata lokaci ne da kuma kashe dukiyar jama'a. Dama can ana tunanen 'yan arewa suna da rauni domin haka idan sun je Abuja ba dole ba ne su tsaya su jajirce akan manufar arewa gaba daya. Akwai hanyoyi da yawa na samun kudi. Misali ma'aikatar Niger Delta ana tura mata kudi da yawa. Haka kuma shirin SURE-P daga rarar kudin man fetur yawancinsu ana karkatasu ne zuwa yankin na Niger Delta. Kasafin kudin kasar an karkata shi can yankin. Yawancin kudaden da kamfanonin hakan man fetur ke biya suna zuwa yankin ne.
Gwamna Rabiu Kwankwaso wakazalika yayi tsokaci game da batun kirkiro jihohi da soke kananan hukumomi da taron ke nemawa matsaya a kansu. Yace batun kirkiro jihohi siyasa ce kawai. Akwai wanda ya ke ganin idan ya tsaya aka kirkiro jihohin zai samu gindin zama musamman a zabe mai zuwa. Kirkiro jihohi da kawar da kananan hukumomi duk tafiyarsu daya. Wato, tare suke. Kirkiro jihohi da kawar da kananan hukumomi ba zasu taimaki zaman lafiya da kwanciyar hankali ba. Kwashewa marashi a karawa maishi ba zai taimaki marashi din ba da ma maishin. Domin duk wadannan abubuwa musamman rashin tsaro nada alaka da irin wannan zalunci na talauta wani bangare a azurta wani.
Dangane da abun da gwamnonin arewa zasu yi su kwato yankin arewa gwamna Kwankwaso yace suna jiran gwamnan Bauchi ya kira taronsu domin su hada kai su kwato yankin daga irin halin da ake neman a jefashi.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.