A wajen babban taron kasa da ake, wasu sun kawo shawarar a rinka yin karba-karba wajen shugabancin kasa, a tsakanin manyan sassan Najeriya guda shida.
Shi yasa muka tuntubi Lauya kuma tsohon dan majalisar dattawa Sanata Abubakar Sodangi, inda yace “wannan nada rauni ga damokradiya.”
Sanata Sodangi, yace a bisa daka ba daidai bane, idan har ana son haka ya tabbata sai an yima kudin tsarin mulkin kasar kwaskwarima, ya kuma kra da cewa yanzu haka shiyoyi shida da ake dashi a kasar baya cikin kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya kuma ce ba lalle bane yankin da shugaban kasa ya fito yafi sauran yankunan kasar samun ci gaba, inda ya bada mulsali da arewacin Najeriya, ganin cewa tafi kowane yankin yawan shuwagabanin kasa kuma itace koma baya.