Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Bauchi Ya Yi Gargadi Ga Sarakuna Da Jami'an Tsaron Dake Hada Kai Da 'Yan Bindiga


Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi).
Gwamnan Bauchi Bala Mohammed (Kauran Bauchi).

Gwamnan jihar Bauchi ya gargadi masu sarautun gargajiya da jami'an tsaron da ake hada baki da su wajen baiwa yan bindiga masu tayar da kayar baya mafaka ko bayanai.

Gwamna Sanata Abdulkadir Bala Muhammed, ya bayyana haka ne a garin Duguri, lokacin da ya ke ci gaba ziyarar jajantawa al'umomin da aka kashe 'yan uwansu dama wadanda aka sace domin kudin fansa.

Kididdiga na nuni da cewar, ana samun yawaitar kashe kashen mutane da kuma sace su, daga yan bindiga a sassan jihar, musamman a yankunan kananan hukumomin Alkaleri da Tafawa Balewa da kuma Ningi.

Yayin da 'yan bindiga ke cin karensu ba bu babbaka, wanda a tsakanin watan Yuni da Yuli an kashe mutane fiye da goma, an kuma sace mutane 17 don kudin fansa, yanzu haka dai wasu daga cikin 'yan uwan wadanda aka sace sun biya kudi sun karbo mutanensu.

A jawabinsa, Gwamna Bala Abdulkadir, ya bayyana alhini game da abubuwan dake faruwa na bakin ciki a jihar, sannan ya ci gaba da cewa suna da labarin masu taimakawa 'yan bindiga dake zaune a cikin duwatsun dake wajen gari, amma yanzu ya bada umarnin a kama duk wanda ke da hannu.

Al'umomin yankunan na ci gaba da mika kukansu ga shugabanni tare da rokon Allah ya sawwake mu su wannan tashin hankali dake addabarsu.

Shugaban karamar hukumar Ningi Mamuda Tabla, ya ce masu satar mutanen sun dauke wa wani dan kabilar Ibo matarsa da jinjiri da kuma kaninsa, sai dai kuma daga baya sun sako matar da jinjirinta.

Domin karin bayani saurari rahotan Abdulwahab Muhammad.

Gwamnan Bauchi Ya Yi Gargadi Ga Sarakuna Da Jami'an Tsaron Dake Hada Kai Da 'Yan Bindiga - 4'01"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00

XS
SM
MD
LG