Gwajin wani magani da ta yiwu ya zama rigakafin cutar COVID-19 na bayyana kyakkyawan sakamako, a cewar kwararru a fannin kimiyya na Amurka da Jamus.
Kamfanin Pfizer da ke Amurka da kamfanin BioNTech na Jamus sun haɗa hannu domin yin aikin da suka yi wa lakabi da “Project Lightspeed,” wanda babban burin shine samar da rigakafin cutar COVID-19.
A ranar Laraba 1 ga watan Yuli duka kamfanonin biyu suka sanar da samun kyakkyawan sakamako daga gwajin wani maganin rigakafi mafi karfi cikin guda 4 da suke aiki akai, wato BNT62b1 wanda ta yiwu ya zama rigakafin cutar.
Wata daya bayan da aka basu rigakafin, wadanda ake gwajin maganin a kansu, jikinsu ya gina garkuwa mai karfi akan coronavirus, daidai ko ma fiye da garkuwar da ke cikin jinin wadanda suka warke daga cutar COVID-19.
Facebook Forum