Sakamakon gwajin gawa, wanda dangin marigayi George Floyd suka sa aka yi, ya nuna cewa shakewa ce ta yi sanadin mutuwarsa a makon jiya, lokacin da wani dan sandan a Minneapolis ya sa gwiwarsa kan wuyan Floyd din.
Dan sandan mai suna Dreke Chauvin ya danne Floyd har na tsawon mintoci da dama.
Floyd, bakar fatan Amurka mai shekaru 46, ya mutu a makon jiya yayin da ankwa ke hannunsa, bayan danne shi din da Chauvin farar fata ya yi.
Mutuwarsa, wadda aka nada ta bidiyo, ta haifar da tashe-tashen hankula a biranen Amurka da dama, inda wasunsu ma suka rikide zuwa na tashin hankali.
Tuni aka tuhumi Chauvin da laifin kisan kai a wannan al’amarin bayan da aka kama shi a radar Juma'a.
Likitan dangin Floyd, Michael Baden, ya ce gabanin mutuwar Floyd bai fama da wata rashin lafiyar da ka iya zama sanadin mutuwarsa.
Wannan rahoton na zuwa ne bayan da binciken wucin gadi da wani likitan Karamar Hukumar Hennepin, ya nuna cewa babu wata alamar cewa shakewa ce ta yi ajalin marigayi Floyd.
Sakamakon binciken na karamar hukumar, ya nuna cewa mutuwar Floyd na da nasaba da yadda ‘yan sanda suka yi da shi, da kuma rashin koshin lafiya.
Facebook Forum