WASHINGTON, DC —
Wakilai Talatin da bakwai a majalisar tarayyar Nigeria, sun bada sanarwar cewa sun fice daga jam'iyyar dake mulki kuma suka yi takara karkashinta sun koma jam'iyyar 'yan adawa, wanda hakan ke zaman wani sabon kalubalen siyasa da nuna yatsa ga shugaba Goodluck Jonathan.
A ran laraba ce, wakilan dake karkashin inuwar jam'iyyar PDP suka bada sanarwar cewa sun chanza sheka zuwa cikin jam'iyyar adawa ta (APC). daukan wannan matakin ya baiwa jam'iyyar Adawa ta APC ta zama mai rinjaye kadan ke nan a majalisar tarayya, wadda ta jima tana karkashin jagorancin jam'iyyar PDP kusan tun shekarar 1999. Sai dai duk da haka, jam'iyyar PDP zata ci gaba da rike matsayinta na shugabar masu rinjaye a Majalisar dattawan Nigeria.