Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Harkar Tsaro Sun Ce Akwai Abin Tayar da Hankali a Wasikar Obasanjo


Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo

Masu kula da harkokin tsaro a Najeriya sun ce babban abinda ya fi tayar musu da hankali shi ne ikirarin da tsohon shugaban yayi cewa gwamnatin shugaba Jonathan tana horas da wasu makasa

A yayin da ake ci gaba da mayarda martini da tayar da kura kan wasikar da tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya rubutawa shugaba Goodluck Jonathan, masana harkokin tsaro sun ce akwai abubuwan da suke tayar musu da hankali sosai a cikin wannan wasika.

Wani tsohon jami’in tsaron farin kaya a Najeriya, Mr. Abraham Jindo, yace babban abin lura shi ne cewa wannan maganar fa ba wai ta fito ne daga bakin wawa ba, ta fito ne daga bakin mutumin da yayi shugabancin Najeriya sau biyu, ya jagoranci rundunar sojojin kasar baki daya, kuma ya san yadda abubuwan kasa ke gudana.

Yace babban abin tayar da hankali shine zargin da Obasanjo yayi cewa shugaba Goodluck Jonathan ya tanadi wasu makasa ana horas da su domin su karkashe ‘yan adawa. Yace idan har hakan ya tabbata gaskiya, to Najeriya tana cikin wani mummunan hadari.

Shi ma masanin tsaro Dr. Abdullahi Bawa Wase, yace biri yayi kama da mutum, domin akwai hujjojin da zasu iya karfafa maganar tsohon shugaba Obasanjo.

Sai dai kuma, wani jigon jam’iyyar PDP a Adamawa, Alhaji Yayaji Gombe, yace zancen na Obasanjo zancen kawai ne domin kuwa babu wanda ya tsunduma kasa cikin masifa kamar sa. Yace yarfiyar siyasa ce, kuma neman bata suna.

Ga rahoton da Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Yola.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00
Shiga Kai Tsaye
TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG