Mahaukaciyar guguwar nan mai lakabin 'Florence,' ta fara addabar yankin gabar jahohin North Carolina da South Carolina a Alhamis da iska da ruwa mai karfi.
Zuwa daren jiya Alhamis, Cibiyar Nazarin Mahaukaciyar Guguwa ta Kasa ta ce guguwar 'Florence' na tazarar kilomita 160 ne kawai daga Wilmington, na jahar North Carolina inda ta ke kada iska mai juyawa kimanin kilomita 155 a sa'a guda.
Kwararru sun yi hasashen cewa guguwar za ta kada zuwa gabar teku a yau dinnan Jumma'a daura da kan iyakar jahohin North Carolina da South Carolina inda karfinta zai ragu zuwa mataki na biyu sabanin mataki na hudu da ta ke kwanaki biyu kawai da su ka gabata.
To amma inda guguwar ke kadawa ne, ba karfin na ta ba, ke firgita kwararru masu hasashe.
Masu hasashen sun ce za a kwarara ruwan inci 101 a wasu sassan North Carolina, kuma hauhawar guguwar za ta kai wajen mita 4 - wato fiye da tsawon gidajen yankin da dama.
Facebook Forum