Majalisar Dinkin Duniya ta kebe ranar goma sha daya ga watan Oktoba ta zama ranar ‘ya’ya mata ta duniya, da nufin daukar matakai kan bukatu da kalubalai da ‘ya’ya mata suke guskanta, tare karfafa masu guiwa su iya cimma gurinsu na rayuwa.
A bana bukin ya maida hankali ne kan taimakawa ‘yara mata su iya tsayawa da kafafunsu kafin fuskantar kalubalar rayuwa, da lokacin da suke cikin wani hali na kunci, da kuma bayan fita wani halin hakula’i. Yau shirin Domin Iyali ya nazarci tasirin wannan ranar a kasashenmu, inda masu kula da lamura suka ce ana amfani da al’ada da addini a tauye hakkokin mata. A wannan makon Shirin ya yi hira da, Barrister Badiha Mu’azu ‘yar gwaggwarmaya kan harkokin mata, da Professer Aisha Abdul daya daga cikin wadanda suka gabatar da Makala a taron da cibiyar nazarin al’amuran jinsi a jami’ar Bayero ta birnin Kano ta shirya domin bukin ranar, da kuma Dr Hawa Balami shugabar kungiyar dake rajin ganin an ba ‘ya’ya mata dama bai daya wadanda suka yi musayar miyau kan wannan ranar.
Facebook Forum