Wani bene mai hawa uku da ake kokarin kammala gina shi ya fadi a Unguwar Kubuwa da ke birnin tarrayyar Najeriya. Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta tabbatar wa Wakiliyar Muryar Amurka, Medina Dauda, cewa mutane bakwai ne faduwar ginin ya rutsa da su, yayinda biyu a cikinsu, suka riga mu gidan gaskiya.
Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Abuja, Alhaji Abbas Idris ya yi karin haske akan gudumawar da hukumar ta bayar a lokacin da wanan bene mai hawa uku ya rufta a Unguwar ta Kubwa da ke Babban Birnin Tarrayya, Abuja.
Benen, wanda aka tsara shi a yanayi na shagunan zamani, wanda ake kira shopping mall a turanci, ana kan gina shi ne a titin Hamza Abdullahi da ke Unguwar ta Kubwa a lokacin.
To yaya kwararru a fanin kimiyyar gine gine ke kallon wannan lamari na faduwar gini tun ana cikin aiki da ke ta faruwa akai akai? Injiniya Ibrahim Babangida ya yi tsokaci kan batun.
A lokacin da ya ke amsa tambayar matakin da Ma'aikatar Birnin Tarayya za ta dauka akan lamarin, Jami'in Ma'aikatar Birnin Tarrayya da ke kula da Ayyuka na Musamman, Attah Ikharo ya yi karin haske da cewa: Ma'aikatar Birnin Tarayya za ta yi cikaken bincike akan rushewar ginin tun daga irin kayayyakin da aka yi amfani da su a lokacin da ake ginin domin a tabbatar cewa an bi doka wajen yin amfani da ingantattun kayan gini da kuma tabbatar da bin umurnin kwararru masu sa ido a gine gine
Ya zuwa lokacin wannan rahoto, jami'an tsaro da jami'an hukumar bada agaji na gaggawa ta Birnin Tarayya suna nan suna aiki domin ganin an ceto dukan wadanda Allah ya kubutar da su daga chikin ginin.
Saurari rahoton Medina Dauda: