Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Kasance Mabuyar ‘Yan Ta’adda Bayan Sun Kai Hare-Hare A Kasashe Makwabta – Masanin Tsaro


Wasu yan ta'adda
Wasu yan ta'adda

A cewar kididdigar zaman lafiya ta duniya ta shekarar 2022, kasar Ghana ce ta biyu a Afirka a jerin kasashe mafiya zaman lafiya bayan Mauritius.

Masana harkokin tsaro sun ba da dalilai daban daban akan abin da ya sa kasar Ghana ba ta fuskatar hare-haren ta’addaci sabanin kasashe makwabatarta.

Wasu sun danganta hakan da yanayin mulki mai kyau; haka kuma wasu suka ce, tsarin matakin tsaro da kasar ta dauka ne, amma Masani a harkokin tsaro kuma shugaban cibiyar tsaron ‘yan Adam da zaman lafiya, Adib Saani, ya bayyana cewa, Ghana ba ta fuskantar hare-haren ta'addanci domin ‘yan ta’addan na amfani da kasar ne a matsayin inda suke haduwa bayan sun kai hari kasashe makwabta.

Masani a kan harkokin tsaro kuma Shugaban Cibiyar Tsaron ‘Yan Adam da Zaman Lafiya ta Jatikay, Adib Saani ya bayyana haka ne a wani taron jama’a mai taken: “Annobar Ta'addanci Tana Barazana ga Tsaro, Kwanciyar Hankali da Ci Gaban Tattalin arzikin Ghana” wanda kungiyar kungiyar NORSAAC, wata cibiya mai zaman kanta da ke wayar da kan al’ummar yankin Arewacin Ghana, ta shirya.

Adib Saani ya ce, ‘yan ta’addan ba su kai wa Ghana hari, ba domin ba za su iya ba ne ko kuma rashin karfin yin hakan, amma domin suna amfani da kasar ne a matsayin mabuya kuma mahadarsu. Ya ce abin da suke yi shi ne, suna kai wa Burkina Faso, Togo da Ivory Coast hari sannan sai su janye zuwa Ghana domin su sake shirya kai wasu hare-haren.

Adib Saani ya gaya wa Muryar Amurka cewa, wata cibiya mai zaman kanta dake Faransa, tare da taimakon wata kungiyar kasar Jamus da kuma rahoto da aka mika wa hukumar tsaron Amurka ne ya sa suka gano wannan bayanin.

Adib Saani ya ce akwai rahoton da aka mika wa Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin duniya a farkon wannan shekarar cewa za a kai hari a Burkina Faso da Togo da Ghana, kuma hakan ya tabbata a wadannan kasashen biyu. Ba su kai wa Ghana hari ba, domin suna amfani da kasar wajen shirye-shiryensu. Kuma sinadarin da suke amfani da shi wajen hada bam dinsu, yawanci a Ghana suke samu. Ya ce, amma tilas ne Ghana ta dauki matakin tsaro ta hanyar karfafa jami’anta da kayan aiki.

Masanin tsaro, Adib Saani ya shawarci gwamnatin Ghana da ta yi amfani da mazauna wuraren da ake tsammanin kasancewar ‘yan ta’addan domin sun san kowa, idan suka ga bako suna ganewa. Sannan kuma a kula da hanyoyin shigowa ta iyakokin Ghana, domin bincike ya nuna cewa akwai barayin hanyoyin 189 a iyakar shiga Ghana daga Burkina Faso.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00

XS
SM
MD
LG