Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Tsaurara Matakan Tsaro A Iyakokin Kasar Bayan Fasa Gidan Yarin Kuje A Abuja


Hukumar Shige da Fice ta Ghana (Wikipedia)
Hukumar Shige da Fice ta Ghana (Wikipedia)

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ghana ta bayar da sanarwa ga dukan kwamandojin shiyyoyi da na sassan kasar da su saka tsauraran matakai a duk iyakokin shiga kasar tare da kara yin sintiri biyo bayan fasa gidan yarin kuje da aka yi a Abuja.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar da sa hannun mataimakin Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Ghana, Laud Ofori Affrifah, hukumar tace mai yiwuwa 'yan Boko Haram da suka tsere daga gidan yarin Kuje, za su yi yunkurin yin hijira zuwa Ghana ta hanyoyin da aka amince da su da kuma haramtattun hanyoyi, idan aka yi "la'akari da yanayin kaura da 'yan Najeriya ke yi zuwa wannan yankin."

Sanarwar tace, "a daren Larabar 6 ga watan Yuli, wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, suka fasa gidan yarin Kuje dake Abuja, inda rahotannin hukuma suka nuna cewa, akalla fursunoni 443 cikin 879 ne suka tsere sakamakon fasa gidan yarin. Daga cikinsu, akwai akalla fursunoni 64 da suke da alaka da kungiyar Boko Haram."

Domin haka hukumar shige da fice na Ghana na sanar da duk kwamandojin shiyyoyi da su dauki tsauraran matakai a duk iyakokin shiga don dakile tare da kame duk fursunonin da za su yi yunkurin kutsawa cikin kasar nan.

A hirar shi da Muryar Amurka, masani a kan harkokin tsaro, Adib Sani, ya ce, ya dace da wannan matakin da hukuomin Ghana ta dauka. Yace, Ghana ce kasa ta farko da za su nemi mafaka sabili da matsayin ci gabanta a yanzu da kuma kasancewarta ana magana da harshen Ingilishi.

Adib Sani ya shawarci hukumomin Ghana da su wayar da kan mazauna iyakokin kasar cewa su kiyaye kuma su sa ido a kan masu shige da fice, kuma masu gidajen haya su binciki duk wadanda suka zo neman hayan gida kafin su ba su.

A ranar 19 ga watar Afrilu 2019, hukumar ‘yan sandan Ghana reshen gundumar Ada da ke yankin Volta, ta kama fursunoni 9 da suka tsere daga gidan yarin Owerri, yayin da suka yi kokarin shigowa kasar ta Kogin Volta.

Saurari cikakken rahoton Idris Abdullah Bako cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG