Keptin ‘yan wasan Ghana Daniel Afiyie ne ya zura kwallayen biyu da suka baiwa kungiyar Black Satellites karkashin jagorancin mai horar da su Abdul Karim Zito kyakkyawar nasara a ranar bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga turawan mulkin mallaka.
Ya zura kwallon ta shi ta farko ne a daidai minti 22 da fara wasan inda ya mari kwallo yayin da aka dauko a gefen gidan ‘yan wasan Uganda.
Bayan minti shida da fara zagayen wasan na biyu ne, dan wasan Accra Hearts of Oak Precious Boah ya turo masa kwallo a kofar gidan Afriyie ya sake zura kwallo ta biyu.
Kungiyar Ghana Black Satelittes ita ce ta biyu a Afrika da ta yi nasarar lashe kofin zakarun Afrika kasa da shekaru 20 sau hudu tare da kasar Misra wacce ita ma ta dau wannan kofin sau hudu, wanda dukkanin su ke bayan Najeriya da ta lashe wannan kofi sau bakwai.
Ghana ta fara lashe wannan kofi ne a shekara 1993 yayin da ta lallasa Kamaru da ci biyu da nema a wasan karshe a kasar Mauritius.
‘Yan wasan Ghana a jagorancin wani tsohon kocinta dan asali Italiya Guisseppe Dosena ta yi wa dadaddiyar kishiyarta Najeriya ci daya mai ban haushi a shekara 1999 a cikin Najeriya inda ta samu kambu na biyu.
Bayan shekaru goma, wani gungun kwararrun ‘yan wasa da Andre Ayew ya yi musu keptin su kuma sun yi nasar da ci biyu da nema a kan Kamaru a Kigali, babban birnin Rwanda.
Shugaban Ghana Nana Akufo-Addo ya mika sakon taya murna ga ‘yan wasan, yana mai jinjina masu da kocinsu kan namijin kokari da suka yi suka lashe wannan kofi.
Shugaba Akufo-Addo ya yi matukar farin ciki da wannan nasara wacce ta zo a ranar 6 ga watan Maris da kasar ta samu ‘yancin kai da cika 64 a yau.