Shugaban ya yi wannan sanarwar ce a wani jawabinsa da aka nuna kai tsaye ta telbijin kasa.
Wannan matakin, ana sa ran zai taimaka wurin dawo da harkokin rayuwa da na tattalin arzikin kasa, zai kuma inganta zirga-zirga tsakanin al’ummar kasashen dake makwabtaka da Ghana.
Shugaban Akufo-Addo ya yi wannan furuci ne yayin da yake bayyana matakan da gwamnatinsa ta dauka na dakile yaduwar cutar covid 19 karo na ashirin da takwas.
Ya ce “daga ranar Litinin 28 ga watan Maris din shekarar 2022 iyakokin kasa da na teku duk an bude su.”
"Matafiya da aka yi wa allurar rigakafin korona na farko da na biyu zasu iya tsallake iyakar kasa da na teku ba tare da anyi musu gwaji ba," inji shi.
Sai dai ya kuma sanar da dage dokar saka takunkumin rufe fuska tare da zuba miliyan 25 na dalar Amurka domin gina makarantar samar da rigakafi.
Tuni dai ‘yan kasuwa da matafiya a Ghana suka yi farin ciki sakamakon sake bude iyakokin da aka kwashe shekaru biyu suna rufe.
Aranar ashirin da daya ga watan Maris din shekarar 2020 ne shugaban ya sanar da rufe iyakokin kasa a yunkurin da gwamnatinsa ke yi na neman dakile yaduwar cutar.
Ga Hamza Adama da karin bayani daga Kumasi: