Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ta Maida Wasu Ayyukan Da ‘Yan China Ke Gudanarwa Hannun 'Yan Kasa


Kumasi, Ghana
Kumasi, Ghana

Gwamnatin Ghana ta sanar da adana kimanin miliyan uku da digo biyar na dalolin Amurka kowane wata a baitul malin kasar biyo bayan yanke shawarar sallamar wasu Chinawa da ke aiki a kamfanin sarrafa makamashin iskar Gas wato Ghana Gas Company

KUMASI, GHANA - Shugaban kamfanin Benjamin Asante, shine ya shedawa manema labarai haka, Ya kuma bayyana cewa, kafin watan Maris din shaikarar 2017 sai wasu Chinisawa su hamsin da biyu ne ke kula da na’urori a kamfanin amma sai aka gano cewa kamata yayi da al’umman kasa su gudanar da wannan aiki.

Dalilin haka suka kulla yarjejeniya da 'yan kasar Chinan da suka amince t su horas da ma'aikatan kasar Ghana su gudanar da ayyukan da takwarorin su na kasar China ke gudanarwa. A yanzu babu ‘dan wata kasa ko daya injiniyoyi dake kula da na’urorin sarrafa iskar gas a kamfanin sai 'yan kasar Ghana.

Shugaban kamfanin ya bayyana cewam tun lokacin da injiniyoyin kasar suka fara wannan aiki kuwa ba'a samu wata matsala ba.

Kumasi, Ghana
Kumasi, Ghana

Wannan mataki da gwamnatin Ghana ta dauka ya farantawa al’umma rai sosai inda mai sharhi bisa harkar sufiri akasar kana tsohon wakilin jamiyyan adawa a zauren majalisan dattawa a Ghana Adam Mutawwakil ya ce wannan matakin baiwa al’umman Ghana dama ya da ce sosai tare da baiwa gwamnati shawara cewa duk wata masana'anta da zata fara aiki kamata ya yi a ringa garwaya ‘yan kasa da baki domin al’umman su ci moriyar albashi.

Masana tattalin arziki kuwa sunce baiwa ‘yan kasa damar zai rage matsalar faduwar darajar sidi bisa dalar Amurka inji Mallam Najeeb Ibn Hassan masanin tattalin arziki.

Ghana dai ta shiga cikin jerin kasashen da ke samar da iskar gas a Afrika ta Yamma amma masana sun ce yawan Gas din da ta samar bai kai yadda zai ishi al’ummar fadin kasar da adadin su ya zarta miliyan talatin ba.

Saurari rahoto cikin sauti daga Hamza Adams:

Ghana Ta Dauki Matakan Mayar Wa ‘Yan Kasa Wasu Ayyukan Da ‘Yan China Suka Mamaye
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG