Kasar Ghana na shirin gudanar da kidayar al'ummar kasarta a karon farko ta hanyar anfani da manhajar na’urar komfuta zallanta.
Wannan zai sa Ghana, wacce zata gudanarda kidayar a cikin watan Maris na shekara mai zuwa, ta shiga layin kasashe irinsu Swaziland, Malawi da Kenya a matsayin kasashen Afrika na farko da zasu gudanar da kidayar jama’a ta irin wannan hanyar.
Har zuwa zaben farko da aka yi a shekarar 2010, ana anfani ne da takarda wajen rubuta sunayen mutane, abinda yasa kirgan jama’a yakan dauki wattani.
Amma a karkashin sabon tsari mai zuwa, Ghana zata yi anfani ne da na’urorin komputa da tauraron Dan Adam wajen tabattar da ganin an kidaya daukacin al'ummar kasar, ba tare da an bar kowa a baya ba.
Facebook Forum